FASSARAR LITTAFIN DALILIN HALITTA (THE PURPOSE OF CREATION) ZUWA YAREN HAUSA.
DALILIN DA YA SA ALLAH YAYI HALITTA. Magana akan dalilin halitta maudu’I ne mai sarkakiya ga kowanne mutum a rayuwarsa/ta. Kowane mutum a so dayawa yakan tambayi kanshi ‘menene dalilin halitta ta?’ ko kuma ‘menene rawar da zantaka a doron kasa?’ Kwayoyin halittar dan Adam da kuma kasar da muke takawa kan nuna cewa, ba kara zube muke ba. Akwai wanda ke da iko akan mu ma’ana (Mahaliccinmu). Tsarin halitta na nuna akwai wanda ya tsara mu. Misali mutum ne yaga sawun kafa kusa da rafi, tunanin sa shine, wani mutuum ya wuce gurin nan ba da dadewa ba. Bai daukar hankali ace ruwan rafi ne ya shigo kan kasa har yabar alamun sawun irin na mutuum ba tare da wani mutuum ne ya wuce wajen ba. Haka ma tunanin mai tunani ba zai taba zama kwakwalwarsa ba cewa an halicce mu ba tare da dalili ba. Kasance war tunanin dan Adam a koda yaushe yana tabbata akan sababi, hakan ne ke sa mutuum tunanin akwai mahaliccinsa kuma akwai dalilan da yasa mahaliccin ya halicce shi. Wannan dalilin ne yasa neman dalilin halittar dan Adam zai sa ya fahimci rayuwarsa kuma ya aikata abunda zai amfaneshi. A tsawon lokuta, so da dama, akwai wasu kadan daga mutane wanda sun sama ransu ba mahalicci. Wai dan Adam kawai ya farune bisa kuskuran kwayoyin duniya.