Ashe bai kamata a ce, ka damu da ka san addinin da aka fi yawan jayayya a kansa a kafafen yaɗa labarai da ke kusa da kai ba?..
Ashe bai kamata a ce, ka ɗan tsaya kaɗan ba, don ka samu cikakkiyar masaniya kuma mai zurfin game da addinin da ya fi kowane addini, aka kuma fi yawan karɓarsa, kamar yadda ƙididdigar duniya ta nuna?..
Ashe bai kamata a ce, kana jin wani irin daɗi ba, a duk lokacin da ka san wani abu game da ilimi, da wayewa, da al’adu, da falsafa da tsarin rayuwar wasu mutane da suke rayuwa tare da mu a wata duniya, da wani addini?
Idan haka ne, me zai hana ka ɗan yi amfani da damar da kake da ita, ka karanta wannan littafi domin ka san tantagaryar abin da addinin Musulunci ya ƙunsa, na gaskiya, wanda aka cirato daga ingantattun tuwasu da asullansa. Sa’annan ka auna su da lafiyayyen hankali da tatacciyar basirarka. Me zai hana?
Idan kuma kana hangen haka ko akwai wani abu mai muhimmanci a cikinsa, ko mai ɗaukar hankali. To, wannan ko shakka babu wannan littafi zai ba ka agaji da gudunmawa ga biyan bukatarka.