Lallai addinin musulunci yana kallon sha'awar dan Adam wanda Allah ya halicce sa da ita a matsayin lalurori wanda ya wajaba a kosar dasu, hasali ma yana daukansa ne abu me kyau wanda akayi umurni dashi matukar ya amfani dashi ta hanyar da Allah ya shar'anta, musulunci baya daukansa akan wani abun kyama wanda ya kamata a gujesa, Allah madaukakin sarki yana cewa: "mun kawata wa mutane so da shawa'ar mata da yara da tarin dukiyoyi na zinari da azurfa da dawakai na kiwo da dabbobi da gonakin noma, wa'innan ababe dukansu ababen more rayuwan duniya ne, shi kuma Allah gareshi makoma da lada me kyau suke (14) " . Suratu al'imran ayata 14