Yaya Wadannan Manzanni Ibrahim, Musa, Isa da Muhammad (Amincin Allah Yatabbata Agaresu) Sukayi Ibada?
Wata rana sheihi; Ahmad Deedat, babban malamin addinin musulunci, ya kai ziyara zuwa garin jidda, dake Saudia Arabiya, ya kuma bada labarin daya daga cikin abinda yayi a rayuwa.
Yace wata rana ya jagoranci taron wasu kiristoci da majusawa (jews) zuwa ziyarar massalaci a garin Durban, dake Africa ta Gudu (South Africa ). Yayin da suka shiga masallacin, shi deedat sai ya cire takalmin sa, ya kuma nemesu da su cire takalmarsu, su bishi.
Sai deedat, ya tambayesu ko sun san menene dalilin cire takalmarku? Sai suka amsa da murya daya cewa “A`a” deedat yayi musu bayani, yace lokacin da Annabi Musa yaje dutsen Sinai, Allah yayi Magana da shi.
Allah yace: “kada ka iso kusa! Ka cire takalminka saboda wannan wajen da kake tsaye wajene mai tsarki” (Exodus 3:5)
Taron mutanen sai suka zauna a benci suna kallo, deedat ya ke6e domin yin alwala. Bayan yagama alwala, sai ya koma ga mutanen yayi musu bayanin abinda yayi. Ya ce wannan abin ba wai shine karshen tsabta ba saboda anayi sau biyar (5) a rana, yana kuma da asali a tarihi, sai ya kara da cewa;
“Musa, Haruna, da ya`yayensu, sunyi amfani da wannan ruwan suka wanke hannayensu da kafafuwansu. Sunayin hakan ne duk lokacin da zasu shiga tanti (tent) domin ganawa cikin bagade (Altar). Musa yabi umarnin Allah. (exodus 40:31-32)
Bayan salloli ta farilla, deedat sai ya koma ga mutanen suna ta kallon sauran musulmai suna sallolin nafilah, sai yayi musu bayanin yadda ake yin sallar, babbar abin shine yin sujuda. Deedat sai yace, haka dukkanin annabawa sukayi ibada yayi nuni ga sujuda. Sai yayi musu qarin bayani da wannan.
Da wuri-wuri, Ibrahim ya yi sujuda goshinsa na ta6a kasa, Allah kuma yasake yimasa Magana. (Genesis 17:3)
Da wuri-wuri, Ibrahim ya durkusa tareda fuskarsa na ta6a kasa. (Genesis 17:17)
Musa da Haruna sun tafi daga wajen taro zuwa ga kofar tanti (tent) domin ganawa. Nan da nan sai suka duqa da fuskokin su na ta6a kasa. Daukakar Allah sai ya bayyana a fuskarsu. (Numbers 20:6)
Kuma Joshuwa ya durkusa da fuskarsa na ta6a kasa yayi bauta…(Joshua 5:14)
Kuma shi (Isa) sai ya qara gaba kadan ya fadi da fuskarsa, yayi bauta (Mattew 26:39)
Deedat da ladabi ya tambayesu wani hanyan bautane yafi kama da kiristiyaniti? Taron kiristoci da majusawar su ka amsa da murya daya sukace “kwarai kuwa hanyar bauta ta musulmai yafi kusa da ta kirista akan saura addinai”
Da yawan kiristocin da suka dawo musulunci a yau, suna shaidawa kan cewa yanzu sun fi zama “kiristoci” na kwarai, Kalmar “kirista” yana nufin “mabiyin yesu kiristi” ko kuma “kirista”. To yaya wadan nan mutanen wanda ke cewa musulmai na ikrarin cewa sune mabiyan yesu na kusa?
Bari muyi tunani da azancin mu, muyi nazarin menene bible yafadi akan Jesus. Misali, idan muka karanta linjila zamuga inda shi Yesu almasiho yayi ibada tareda goshin shin a ta6a kasa, ya gaida mabiyansa wanda sukayi Imani da shi da nuni ta aminci kuma yayi azumi na lokaci mai tsawo.
Hakika dayawan kiristoci da suka koma musulunci sun shaida cewa su dai musulmai ne a kalma kafin su gano matabbaciyar imanin su cikin littafi mai girma watau al-qurani wanda aka saukar ga annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata gareshi)
“yaku wanda kukayi Imani, ku dukursa da sujuda domin bauta ga ubangijinku kuma kuyi aiki na kwarai ko kwa rabauta” (Noble Qur`an 22:77)
Kaga hanyar dan Adam ta kaddarawar tauhidi bai rarabuwa daga asali. A yau wasu mutane sunyi ikrarin cewa su mabiyane na hanyar Isa, Ibrahim da Musa (amincin Allah shi tabbata a garesu) amman sun bar kan hanya. Ga kiristiyaniti, wasu mutane bisa ga kuskure sun kirkiri wata cikakkiyar sabuwar addini akan Annabi Isa wanda hakan ya mayar da shi wani abunda shi bai ta ba ikrarin hakan ba.
Yanzo ka tambayi kanka da gaskiya, wanene hakikanin mai bin misalin Isa a yau ? kamar yadda watakila ka sani, musulmai suna sallah tareda goshinsu na ta6a kasa, aqalla sau biyar a rana.
Musulmai na bin addinin Isa; Addinin da yayi magana yakuma aikata. Kamar haka, musulmai keyin bautar Allah wanda Isa ya bautawa; shi ne Ibrahim, Musa, da Muhammad tsira da amincin Allah shi tabbata a garesu.
Kuma, musulmai ko yaushe suna gaida yan uwansu da Kalmar “Aminci shi tabbata a gareka” qari akan hakan Isa yayi azumin kwana arba`en (40) a cikin daji, musulmai suna azumin wata guda a cikin watan ramadana.
Akarshe, bari mu kaskantar da kanmu muyi ibada kamar yadda dukannin annabawa sukayi, za`aiya saukarwa daga (salah) book daga shafin mu ta yanar gizo.